Nigeria ta samu tattaunawa da Binance domin shigo da Crypto Nigeria 🇳🇬
Gwamnatin Nigeria tana kan Tattaunawa da Hukumar Babbar Kasuwar hada-hada ta Taurarin Sulalla wato Binance kan yadda za'a samu shigo da harkar Crypto izuwa Nigeria gadan-gadan
Tun a watan Fabrairu na Shekarar 2021 ne Babban Bankin Kasar Nigeria 🇳🇬 ya haramta harkar Taurarin Sulalla a Nigeria yayinda hakan kuma ya sa'ba da ra'ayin Yan Majalisu da kuma Ma'aikatar dake kula da Fannin Sadarwa da Tattalin Arziki na Yanar Ankabuti karkashin Jagorancin Ministan Farfesa Isa Ali Pantami.
a yanzu haka dai Farfesa Isa Ali Pantami yana kokarin habaka Nigeria da kuma Matasan wannan kasa abisa wannan fanni don ganin cewar sunada budewar ido a fannin kuma suna samun Arziki ta yadda zasu kawowa kasar cigaba da magance rashin aikin yi da kuma dauke talauchi a kasar cikin wasu yan shekaru kadan masu zuwa, a yanzu dai haka Nigeria zata amince da harkar Crypto na Taurarin Sulalla kuma za'a kokarta wajen agazawa matasa don a kara musu sani da kuma tallafi abisa tsarin, yanzu haka ana kan tattaunawa don ganin yadda lamarin zai kasance a kasar ta Nigeria.
Crypto Hausa



0 Comments